Bidiyon yadda Hukumar Hisba ta zane ƴan daudun da suka yi shigar mata a jihar Kano
Kotun Shari’ar Addinin Musulinci dake zaman ta a Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta yankewa, wasu yan Daudu Hukunci, bayan sun yi shigar mata dan yin rawar karya kwankwaso a wajen bikin uban gidansu.
Mai shari’ar ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar naira dubu goma-goma kowannen su, tare da yi musu Bulala goma-goma.
Mukaddashin Kwamandan Hukumar Hisbah na Jahar Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar , ya bayyana cewa hukumar ba zata gajiya ba , wajen dakile aiyukan Badala , domin aikin hukumar shi ne ,yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.


0 Comments