Daraktoci sun daina saka ni a film saboda haka aure kawai zan yi—Maryam Booth













Daraktoci sun daina saka ni a film saboda haka aure kawai zan yi—Maryam Booth

Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Booth ta koka tare da nuna Ι“acin ranta kan yadda kusan illahirin daraktocin Kannywood suka haΙ—e mata kai gaba Ι—aya sun daina saka ta a cikin shirin Film saboda haka da zarar ta samu miji aure kawai za tayi ta huta kamar yadda ta bayyana Ι—azu


Shahararrinya jarumar fina finan Hausa na Kannywood Maryam Booth ta bayyana cewa darektochi sun daina sakani a Fim, Babu abin da zan zaba, Aure kawai zanyi na zauna a gidan mijina

Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Booth, wacce mahaifiyarta Allah ya yi mata rasuwa a kwanan nan Zainab Booth ta shaidawa kafafen yaΙ—a labarai dalilin da yasa masu shirya fina-finai (Producers) suka daina sakata a cikin fina-funan su.

Jarumar ta alaΖ™anta hakan da bayyanar bidiyon tsiraicinta a shekarun baya kamar yadda Neptune Prime ta ruwaito.

“Tun ina Ζ™arama na kasance ina fitowa a fina-finan Kannywood, saboda mahaifiyata Hajiya Zainab Booth(Allah ya saka mata da gidan Aljanna) ta daΙ—e a cikin masana’antar, don haka ban taba daina fitowa a fina-finai haka kawai ba.

Amma tunda wani matashi da ake Ζ™ira Dezeel wanda ya yi ikirarin cewa saurayina ne ya bayyana hotunan tsiraici na a kafafen sada zumunta, yanzu mutane na yi min kallon Ζ΄ar isaka mara tarbiyya”. In ji ta.

Post a Comment

0 Comments