Manyan mutanen da suka yi magana kan jefa wa fararen hula bam a Kaduna
Al'umma da Ζ΄an siyasa da Ζungiyoyin addinin musulunci a Najeriya suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bayan harin da sojoji suka kai "bisa kuskure" a Tudun Biri, wani Ζauye a Ζaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a arewacin Ζasar.
Harin dai ya yi sanadin asarar rayuka da dama tare da jikkatar wasu da ke samun kulawa a asibiti.
Hukumomi sun bayyana cewa mutane 85 ne harin ya kashe, sai dai Ζungiyoyi masu zaman kansu da kuma al'ummar Ζauyen na cewa adadin ya zarce haka.
Ga wasu daga cikin manyan mutanen da suka yi tsokaci game da lamarin:


0 Comments