Dangote Ya FaΙ—o Daga Matsayin Attajirin Da Yafi Kowa Kudi A Africa












Dangote Ya FaΙ—o Daga Matsayin Attajirin Da Yafi Kowa Kudi A Africa


Mujallar Forbes da ke bibiyar harkokin masu arziΖ™in duniya, ta ce a yanzu hamshaΖ™in biloniyan nan Ι—an Ζ™asar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ne mutumin da ya fi kowa kuΙ—i a Afirka.

Hakan na nufin Johann Rupert mai shekara 73, ya kere attajirin Ι—an kasuwa na Najeriya, Aliko Ɗangote a yawan arziki wanda a baya yake riΖ™e da matsayin.

A alΖ™aluman da Forbes ta fitar na baya-bayan nan, a kan arzikin attajirai a kowacce rana, darajar arzikin Johann Rupert ta kai dala biliyan 10, yayin da Aliko Dangote aka Ζ™iyasta nasa arzikin a kan dala biliyan 9.7.

Aliko Dangote, mai shekara 66, ya koma mataki na biyu a jerin masu arzikin Afirka bayan da dukiyarsa ta yi Ζ™asa daga dala biliyan 13.5 zuwa dala biliyan 9.5 a farkon shekarar 2024.

Mujallar ta nuna cewa an samu raguwar kuΙ—in hamshaΖ™an Ζ΄an kasuwa kamar Rabiu Abdussamad da darajar arzikinsa ya kai dala biliyan 5.7 da Mike Adenuga wanda nasa arziΖ™in ya kai dala biliyan 3.1.

Bayanai na cewa raguwar darajar arzikin nasu, ba zai rasa nasaba da yadda darajar naira ke ci gaba da faΙ—uwa ba, da kuma wasu matsaloli da suka shafi tattalin arziki

Post a Comment

0 Comments