An ga watan azumin Ramadan a Najeriya











An ga watan azumin Ramadan a Najeriya



Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a Najeriya.Hakan na nufin gobe Litinin za ta kasance 1 ga watan Ramadan, wato ranar da al'ummar Musulmi a duka sassan ƙasar za su tashi da azumin wannan shekara.Ƙasashe da dama sun sanar da ganin watan na azumi a yau, ciki har da Saudiyya.Ya yi kira da a yi wa ƙasa addu'a, musamman a daidai wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa da kuma matsalolin tsaro.

Post a Comment

0 Comments