An sake naΙa Sheikh Yasir Ad Dawsary a matsayin babban limamin Masallacin Harami na Makkah.
Sheikh Dawsary, wanda aka naΙa shi bisa umarnin Shugaban Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami guda Biyu, Sheikh Abdul Rahman As Sudais, zai kwashe shekaru 4 a kan muΖamin.
Hakazalika, ofishin ya kuma naΙa Sheikh Ahmad Al Hudaify da Sheikh Khalid Al Muhanna a matsayin manyan limaman Masallacin Ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallama a Madina, su ma na tsawon shekara 4.


0 Comments