Wata mata ta biyawa kishiyarta aikin Hajji a jihar Nassarawa
Labarin matar data biyawa kishiyarta kujerar aikin Hajji da kuΙin ajiye aikinta ya ja hankalin mutane a ciki da wajen jihar, Nasarawa inda dubban jama'a suke ta yi mata fatan alheri da gamawa lafiya, matar tace wallahi zaman lafiyar da suka shafe shekaru suna yi da juna ne yasa ta biya mata Makka ba'a taΙa jin kansu ba kowa na zaune da kowa da zuciya Ιaya
Ita ma wacce aka biya mawa tace wallahi abin ya bata mamaki kuma dama ta faΙa mata cewa da zarar an biyata kuΙin ajiye aiki zata biya mata aikin Hajji sai gashi ta cika alΖawari, muna fatan Allah ya saka mata da Alheri ya bamu mata nagari
Kunji fa menene ra'ayoyinku shin kuna ganin za'a iya samun macce kishiya irin wannan a garinku?


0 Comments